Benjamin Mendy: An tuhumi dan wasan Manchester City da zargin fyade

Benjamin Mendy

Asalin hoton, PA Media

Bayanan hoto,

Ana ci gaba da tsare Benjamin Mendy

Ana tuhumar mai tsaron bayan Manchester City, Benjamin Mendy da laifi hudu da ya shafi fyade da kuma cin zarfi.

'Yan Sandan Cheshire ne suka tuhumi dan wasan mai tsaron baya, mai shekara 27.

Tuhumar ta kunshi korafi uku kan wata 'yar shekara 16 da ake zargin ya aikata laifin tsakanin Oktoban 2020 da Agustan shekarar nan.

Ana ci gaba da tsare Mendy, wanda ake sa ran gurfanar da shi a kotun Chester ranar Juma'a.

Mendy mai tsaron baya ya koma Manchester City daga Monaco kan fam miiyan 52 a 2017.

Manchester City ta sanar da dakatar da Mendy wanda ya buga wa tawagar Faransa Tamaula, har sai an kammala bincike.

Kungiyar ta Etihad ta ce ''Batun yana kotu, kuma ba za ta iya cewa komai ba, har sai an kammala bincike.''