Joaquin Correa: Inter Milan ta daukI aron dan wasan Lazio

Joaquin Correa

Asalin hoton, Inter Milan FC

Bayanan hoto,

Joaquin Correa ya buga wasa 38 a bara a dukkan fafatawa da cin kwallo 11 da bayar da shida aka zura a raga

Inter Milan ta kammala daukar aron dan kwallon tawagar Argentina, Joaquin Correa daga Lazio.

Kamar yadda kungiyoyin da ke buga Serie A suka sanar ranar Alhamis, Inter za ta iya mallakar dan kwallon idan ya taka rawar gani.

Lazio ta ce ta bayar da aron dan wasan kan Yuro miliyan 5.87, kuma Inter za ta sayi dan kwallon fam miliyan 25 idan tana son ya ci gaba da zama a kungiyar.

Inter ta sanar cewa Correa ya saka hannu kan yarjejeniyar da za ta kare a Yunin 2025, kuma mai shekara 27 zai iya buga wa Inter karawar Serie A da za ta je Verona ranar Juma'a.

Correa wanda ya buga wasa 38 a bara a dukkan fafatawa da cin kwallo 11 da bayar da shida aka zura a raga, zai sake taka leda karkashin tsohon kocin Lazio, Simone Inzaghi.

Inter mai rike da Serie A, tana kan teburi a mataki na daya, bayan da ta ci Genoa 4-0 a wasan makon farko da bude babbar gasar Italiya ta bana.