Champions League: Man City za ta kara da PSG, Chelsea da Juventus

Asalin hoton, Getty Images
Mai rike da kofin Premier League, Manchester City tana rukuni da ya hada da Paris St-Germain da RB Leipzig da kuma Club Bruges a gasar Champions League ta bana wasannin cikin rukuni.
Mai rike da kofin Zakarun Turai, Chelsea tana rukunin da ya hada da Juventus da Zenit St Petersburg da kuma Malmo ta Sweden..
Manchester United za ta kara da Villarreal, wadda ta doke ta a wasan karshe a Europa League a bara, suna rukuni tare da Atalanta da kuma Young Boys.
Liverpool kuwa tana rukunin da ya hada da Atletico Madrid da FC Porto da kuma AC Milan.
Yadda aka raba jadawalin gasar Champions League:
Rukunin A: Manchester City da Paris St-Germain da RB Leipzig da kuma Club Bruges
Rukunin B: Atletico Madrid da Liverpool da Porto da kuma AC Milan
Rukunin C: Sporting Lisbon da Borussia Dortmund da Ajax da kuma Besiktas
Rukunin D: Inter Milan da Real Madrid da Shakhtar Donetsk da kuma Sheriff Tiraspol
Rukunin E: Bayern Munich da Barcelona da Benfica da kuma Dynamo Kyiv
Rukunin F: Villarreal da Manchester United da Atalanta da kuma Young Boys
Rukunin G: Lille da Sevilla da FC Salzburg da kuma Wolfsburg
Rukunin H: Chelsea da Juventus da Zenit St Petersburg da kuma Malmo
Wasan karshe na Champions League a bana za a yi ne a filin wasa na St Petersburg a Rasha ranar Asabar 28 ga watan Mayu.