Cristiano Ronaldo: Man Utd na gab da sayen dan kwallon Juventus

Ronaldo celebrates scoring against Manchester City in 2007

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ronaldo ya shafe shekaru shida a Old Trafford kafin ya koma Real Madrid a 2009

Manchester United ta ce ta cimma matsaya da Juventus domin sayen dan kwallon Portugal Cristiano Ronaldo.

United ta ce kammala cinikin ɗan wasan da ya lashe Ballon d'Or sau biyar ya ta'allaƙa ne da batun abin ɗan wasan yake so da kuma batun samun biza da kuma lafiyarsa.

A wani saƙo da Manchester United ta wallafa a shafinta na Twitter, ta ce "maraba da zuwa gida Ronaldo," wadda wannan alama ce da ke nuna cewa Ronaldo zai koma kulob ɗin

Ronaldo ya ci ƙwallo 118 a wasanni 292 da ya buga a lokacin da yake Old Trafford kafin daga baya ya koma Real Madrid.

A baya dai kocin Juventus, Massimiliano Allegri ya tabbatar da cewa Ronaldo ya ce "bai da niyyar ci gaba da murza leda" tare da Juventus.

Ronaldo ya kulla yarjejeniya da Manchester United daga Sporting Lisbon a kan fiye da fan miliyan 12 a shekara ta 2003 inda ya zura kwallo 118 cikin wasa 292 a kulob din.

Sanarwar da United ta yi na zuwa ne kwanda guda bayan da Manchester City ta nemi agent ɗin Ronaldo Jorge Mendes