Kurt Zouma: West Ham na gab da kulla yarjejeniya da dan kwallon Chelsea

Kurt Zouma playing for Chelsea

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kurt Zouma ya bugawa Faransa kwallo sau takwas

West Ham na gab da sayen dan kwallon Chelsea Kurt Zouma a kan fan miliyan 25.

Kocin West Ham, David Moyes na kokarin kara karfin tawagarsa a yayin da za su buga gasar kwallon Turai.

Zouma mai shekaru 26, an gwada lafiyarsa a Hammers kuma ya kusa ya kamala kula yarjejeniya da kulob din.

"Chelsea ta amince da tayinmu a kan Kurt amma ba a kammala gwada lafiyarsa ba," in ji Moyes.

Dan kwallon na Faransa ya bugawa Chelsea wasa 36 a kakar wasan da ta wuce amma kuma ba ya cikin wadanda ke da makoma a karkashin Thomas Tuchel.

"Ana tattaunawa tsakanin West Ham da Chelsea a kan Kurt," in ji Tuchel.

Zouma ya koma Chelsea ne a shekara ta 2014 daga Saint-Etienne.