Lionel Messi na daf da shafe tarihin da Pele ya kafa

Asalin hoton, Getty Images
Messi ya fara yi wa babbar tawagar Argentina tamaula cikin 2005 ya ci kwallo 76 kawo yanzu
Brazil za ta karbi bakuncin Argentina ranar Lahadi a rukunin kudancin Amurka na neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya.
Kyaftin din Argentina, Messi wanda ya fara yi wa babbar tawagar kasar tamaula a cikin shekarar 2005 ya ci kwallo 76 kawo yanzu a karawa 152.
Tsohon zakakurin dan wasan Brazil, Pele wanda ya bar taka leda kusan shekara 50, shine ke rike da tarihin yawan zura kwallaye a Kudancin Amurka mai 77 a raga.
Kusan mako tara kenan da Brazil da Argentina suka ffafata a wasan karshe a Copa America, inda Argentina ta yi nasara da ci 1-0.
Wannan shine wasa takwas-takwas da kowacce tawaga za ta buga a rukunin Kudancin Amurka domin neman neman gurbin kai wa gasar cin kofin duniya da za a yi a Qatar a 2022.
Wasan da suka kara ranar Lahadi bana cin kofin bane, kuma ba shine zai fayyace wadda za ta samu gurbin shiga gasar kofin duniya ba, illa dai na hamayya ne, kowacce za ta yi kokarin kare martabarta a fannin kwallon kafa.
Tuni kocin Argentina, Lionel Scaloni ya sanar cewar Messi zai buga fafatawar duk da ketar da aka yi masa a karawar da suka doke Venezuela 3-1 ranar Juma'a.
A kuma ranar ce Brazil ta yi nasara a gidan Chile da ci 1-0, kuma Everton Ribeiro ya ci mata kwallon.
Tawagar Brazil ce ke jan ragamar teburin kudancin Amurka da maki 21, sai Argentina mai maki 15, sannan Ecuador ta uku mai maki 12, sai Uruguay ta hudu da maki 9.
Sauran wasannin da za a buga ranar Lahadi:
- Ecuador da Chile
- Paraguay da Colombia
- Uruguay da Bolivia