'Yan Super Eagles da ke Birtaniya ba za su buga wasan Cape Verde ba

Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Ranar Talata Najeriya za ta buga wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da Cape Verde, karawar nahiyar Afirka.

Super Eagles ta yi nasarar doke Laberiya da ci 2-0 ranar Juma'a a Legas, inda Kelechi Iheanacho ya ci mata kwallayen a wasan farko na cikin rukuni na uku.

Sai dai kuma 'yan wasan da ke Super Eagles masu taka leda a Birtaniya sun bar sansanin su da ke Eko otal and Suites a Legas zuwa kungiyoyin su ranar Asabar.

Wadanda suka koma kungiyoyin su sun hada da Wilfred Ndidi da Kelechi Iheanacho da Alex Iwobi da Oghenekaro Etebo da William Troost-Ekong da Joe Aribo da kuma Leon Balogun.

'Yan wasan na Ingila ba za su iya zuwa Cape Verde taka leda ba, bayan da gwamnatin Birtaniya ta ayyana kasar a matakin wurin da ke da hadarin kamuwa da cutar korona.

Hakan na nufin duk wanda ya je kasar da Birtaniya ta ayyana da hadarin kamuwa da annobae, ya zama wajibi ka killace kai kwana goma idan ka koma Birtniya.

Wannan kwanakin zai hana wasu 'yan kwallon buga wa kungiyoyin su wasa biyu a Premier League da daya a gasar Zakarun Turai.

Tuni dai wasu kungiyoyin Premier League suka hana 'yan wasa da dama zuwa buga wa kasashen su tamaula, wadanda aka ayyana masu hadarin kamuwa da cutar ta Korona.