Real Madrid za ta yi wasa shida cikin watan Satumba

Real Madrid FC

Asalin hoton, Real Madrid FC

Bayanan hoto,

Real Madrid ta yi wasa uku a waje a jere tana mataki na daya a kan teburin La Liga da maki bakwai

A karshen makon nan za a ci gaba da wasannin gasar kasashen Turai, inda Real Madrid za ta yi karawa shida a cikin watan Satumba.

Cikin fafatawar da za ta yi biyu daga ciki a Champions League za ta kara da Inter Milan da kuma FC Sheriff Trispol ta Rasha.

Sauran wasa hudu kuwa a La Liga za ta yi da ya hada da Celta Vigo da Valencia da Mallorca da kuma Villareal.

Real Madrid wadda ta yi wasa uku a kakar bana a La Liga ta je ta doke Real Betis 1-0 ranar Asabar 28 ga watan Agusta.

Tun kan nan Real ta fara buga gasar La Liga ta bana da cin Alaves 4-1 ranar Asabar 14 ga watan Agusta, sannan ta tashi 3-3 a gidan Levante ranar Lahadi 22 ga watan Agusta.

Real wadda ta buga wasa uku a bana a La Liga a waje, za ta karbi bakuncin Celta Vigo ranar Lahadi 12 ga watan Satumba, lokacin dukkan 'yan wasa sun koma kungiyoyin su bayan buga wa kasashen su wasannin shiga gasar kofin duniya.

Real Madrid tana mataki na daya a kan teburin La Liga da maki bakwai, bayan wasa uku, sauran masu maki bakwai-bakwai sun hada da Sevilla da Valencia da Barcelona da kuma Atletico Madrid mai rike da kofin bara.

Ga jerin wasa shida da Real Madrid za ta fafata cikin watan Satumba:

Gasar La Liga ranar Lahadi 12 ga watan Satumba

  • Real Madrid da Celta Vigo

Champions League ranar Laraba 15 ga watan Satumba

  • Inter Milan da Real Madrid

Gasar La Liga Lahadi 19 ga watan Satumba

  • Valencia da Real Madrid

Gasar La Liga Laraba 22 ga watan Satumba

  • Real Madrid da Mallorca

Gasar La Liga Asabar 25 ga watan Satumba

  • Real Madrid da Villarreal

Champions League Talata 28 ga watan Satumba

  • Real Madrid da FC Sheriff