Italiya ta kafa tarihin wasa 36 a jere ba a doke ta ba

Roberto Mancini

Asalin hoton, Getty Images

Tawagar kwallon kafa ta Italiya ta kafa tarihin yin wasa 36 a jere ba tare da an doke ta ba.

Italiya ta yi wannan bajintar bayan da ta tashi 0-0 a gidan Switzerland a wasan neman shiga gasar cin kofin duniya a jiya.

Tawagar ta yi nasarar lashe kofin nahiyar Turai wato Euro 2020 a cikin wannan bajintar, inda ta doke Ingila a wasan karshe a Wembley cikin watan Yuli.

Ranar Alhamis Italiya ta tashi 1-1 da Bulgaria a wasan neman shiga gasar cin kofin duniya, wasa na 35 kenan a jere ba tare da yin rashin nasara ba.

Hakan ne ya sa Italiya ta yi kan-kan-kan da tawagar Brazil da ta Sifaniya masu tarihin yin fafatawa 35 a jere ba a doke su ba.

Rabonda a doke tawagar Italiya tun ranar 10 ga watan Satumbar 2018 a wasan Uefa Nations League da Portugal ta yi nasara a kanta.