An soke karawar Brazil da Argentina kan batun tsoron yada cutar korona

Brazil-Argentina was halted after covid health regulation issues

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

'Yan wasan Argentina sun fice daga filin, bayan da jami'an lafiya na Brazil suka yi shirin tsayar da fafatawar

'Yan wasan Argentina sun fice daga fili a karawa da Brazil a wasan shiga gasar kofin duniya, kan 'yan kwallon da suka karya dokar killace kai.

Argentina ta fice daga filin wasan, bayan da jami'an lafiya na Brazil suka shiga filin suka dakatar da karawar ta hamayya.

Hakan ya biyo bayan da jami'an lafiya suka ce ya zama wajibi 'yan wasan hudu daga Argentina da ke taka leda a Ingila sai sun killace kan su.

Koda yake ba su fayyace 'yan wasan ba, sai dai masu buga Premier League daga Argentina sun hada da Emiliano Buendia da Emiliano Martinez da ke wasa a Aston Villa, sai Giovani lo Celso da Cristian Romero na Tottenham.

Kuma Argentina ta fara karawar da Martinez da Lo Celso da kuma Romero a wasan da aka tsara yi a Sao Paulo.

Kamar yadda aka tanadi dokar, duk wanda ya je Birtaniya, sannan ya koma Brazil kafin mako biyu, sai ya killace kansa kwana 14.