Abinda ya kamata ku sani kan wasan Barca da Bayern ran Talata

Champions League

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Chelsea ce ke rike da Champions League, bayan da ta ci Manchester City ta kuma lashe UEFA Super Cup

Barcelona za ta karbi bakuncin Bayern Munich a wasan farko na cikin rukuni na biyar a gasar Champions League ranar Talata.

A wannan karon Barcelona za ta buga wasan ba tare da Lionel Messi ba, wanda ya koma taka leda a Paris St Germain a bana.

Messi shine na biyu a yawan cin kwallo a Champions League mai 120 a raga, bayan Cristiano Ronaldo mai 135 kawo yanzu.

Wasa na karshe da suka kara a tsakaninsu shine ranar 14 ga watan Agustan 2020 a Porto, lokacin da suka yi karawa daya a Porto, sakamakon hana yada cutar korona, inda Bayern Munich ta ci 8-2.

Wadanda suka ci wa Bayern kwallaye sun hada da Ivan Perisic da Serge Gnabry da Joshua Kimmich da Robert Lewandowski da Philippe Coutinho da kuma Thomas Muller da kowanne ya ci bibiyu.

Ita kuwa Barcelona ta ci kwallon farko ta hannunn David Alaba wanda ya ci gida da kuma Luis Suarez da ya zura daya a ragar Bayern.

Kungiyar Jamus da ta Sifaniya sun lashe Champions League guda 11 a tsakaninsu, inda Bayern take da guda shida, ita kuwa Barcelona guda biyar ne da ita kawo yanzu.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Kofi na karshe da Bayern ta lashe shine na kakar 2019/20, wanda ta yi nasaka a kan Paris St Germain, ita kuwa Barcelona rabonta da Champions League tun kakar 2014/15, bayan da ta doke Juventus 3-1.

Fafatawar da Barcelona ta buga da Bayern Munich ya kai 11, inda kungiyar Camp Nou ta ci wasa biyu da canjaras biyu aka doke ta sau bakwai.

Haka kuma Barcelona ta ci kwallo 16 a ragar kungiyar Jamus, ita kuma aka zura mata 26.

Amma a wasan Champions League kadai Barcelona ta ci karawa biyu da canjaras daya, Bayern ta yi nasara a shida, Barcelona ta ci kwallo 13 aka zura mata 22 a raga.

Jerin wasa tsakanin Barcelona da Bayern Munich:

1995/95 UEFA Cup wasan daf da karshe

Bayern Munich 2 - 2 Barcelona

Barelona 1 - 2 Bayern Munich

Bayern ta kai zagayen gaba da ci 4-3 ta doke Bordeaux a wasan karshe

1998/99 Champions League rukuni na hudu

Bayern Munich 1 - 0 Barcelona

Barcelona 1 -2 Bayern Munich

Bayern Munich ta kai zagayen gaba, wadda ta yi rashin nasara a hannun Man United a wasan karshe

2008/09 Champions League Quarter Final

Barcelona 4 - 0 Bayern Munich

Bayern Munich 1 - 1 Barcelona

Barcelona ta kai zagayen gaba da ci 5-1 ta kuma yi nasara a kan Man United a wasan karshe

2012/13 Champions League wasan daf da karshe

Bayern Munich 4 - 0 Barcelona

Barcelona 0 - 3 Bayern Munich

Bayern Munich ta ci kwallo 7-0 ta kuma doke Dortmund a karawar karshe

2014/15 Champions League wasan daf da karshe

Barcelona 3 - 0 Bayern Munich

Bayern Munich 3 - 2 Barcelona

Barcelona ta kai zagayen gaba da ci 5-3 ta kuma ci Juventus a wasan karshe

2019/20 Champions League Quarter Final

Barcelona 2 - 8 Bayern Munich

Bayern Munich ta yi nasara a kan PSG a fafatawar karshe