Young Boys da Manchester United: Ronaldo zai buga wasan ran Talata

Edinson Cavani

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wasa daya kacal Edison Cavani ya buga wa Manchester United a kakar bana

Cristiano Ronaldo yana cikin 'yan wasan Manchester United da za ta kara da Young Boys ranar Talata a Champions League.

United za ta ziyarci Young Boys domin buga wasan farko a cikin rukuni a gasar Champions League ta bana.

Sai dai kungiyar ba za ta je wasan da Edison Cavani, sakamakon jinya da yake yi, wanda bai buga mata wasan Premier League ranar Asabar ba.

Dan kwallon tawagar Uruguay ya ji rauni ne a lokacin atisayen tunkarar karawa da Newcastle United, wanda United ta ci 4-1 a karshen mako.

Sai dai Ole Gunnar Solskjaer ya hada da matashin dan wasa Anthony Elanga cikin 'yan wasa 22 da zai je Old Boys har da mai tsaron raga Matej Kovar.

Ronaldo, kyaftin din Portugal ya ci kwallo biyu a wasa da Newcastle, wanda zai buga mata Champions League a karon farko tun bayan da ya bar Old Trafford a 2009.

'Yan wasan Manchester United da ta je Old Boys da su:

De Gea da Heaton da Kovar da Bailly da Dalot da Lindelof da Maguire da Shaw da Varane da Wan-Bissaka da Fernandes da Fred da kuma Lingard.

Sauran sun hada da Mata da Matic da Pogba da Sancho da Van de Beek da Elanga da Greenwood da Martial da kuma Ronaldo.