Ko Bayern Munich za ta kara ragargazar Barcelona kuwa?

Champions League

Asalin hoton, Getty Images

Barcelona za ta karbi bakuncin Bayern Munich a wasan farko na cikin rukuni na biyar a gasar Champions League ranar Talata.

Ranar 14 ga watan Oktoban 2020 Bayern Munich ta doke Barcelona 8-2 a Porto a wasan daf da na kusa da na karshe da suka yi karawa daya don gudun yada cutar korona.

Kungiyar Sifaniya za ta karbi bakuncin ta Jamus a wasan farko a bana da zai fayyace ko Barcelona za ta yi nasara ko za ta kara barin a sharara mata kwallaye da yawa a matakinta na babbar kungiya a fannin tamaula.

Tun bayan da suka kara a Portugal an samu sauye-sauye a Barcelona, wadda ta dauki sabbin 'yan wasa, wadda take fama da matsin tattalin arziki.

Halin da Barcelona ta shiga ya sa ta rabu da zakakurin dan wasanta Lionel Messi wanda yanzu yana taka leda a Paris St Germain a matakin wanda kwantiraginsa ya kare a Camp Nou a karshen kakar bara.

Messi ya ci kwallo 120 a Champions League a Barcelona shine na biyu a yawan zura kwallaye a raga a gasar zakarun Turai, bayan Cristiano Ronaldo na Manchester United.

Masu ci wa Barcelona kwallo a karawar da Bayern Munich ta ci 8-2, sun hada da Luis Suarez da kuma Antoine Griezmann, wadanda yanzu haka suna buga wa Atletico Madrid tamaula.

Philippe Coutinho, wanda ya buga wasannin aro a Bayern Munich a kakar 2019/20, wanda ya ci kungiyarsa kwallo biyu a takwas din da kungiyar Jamus ta ci, yanzu yana Barcelona.

Barcelona za ta buga karawar da sabon dan wasa Memphis Depay, wanda ke taka rawar gani tun fara kakar bana a kungiyar.

Watakila dan kwallon da ta dauka aro Yusuf Demir ya buga mata wasan, bayan da matasanta Ousmane Dembele da kuma Ansu Fati ke jinya, ba za su buga wasan na ranar Talata ba.

Shima sabon dan wasan da ta dauka a bana Sergio Aguero da kuma Martin Braithwaite ba za su buga mata wasan na Champions League ba, hakan zai sa Luuk de Jong ya samu damar buga wa Ronald Koeman fafatawar ta Camp Nou.

Barcelona ta samu hutu ba ta buga gasar La Liga da Sevilla ba a karshen mako da hakan ya ba ta damar shirin da take bukata.