Kasuwar 'yan kwallo: Bellingham da Rice da Werner da Pogba da kuma Lingard

Jude Bellingham

Asalin hoton, Getty Images

Sai kungiya ta tanadi sama da yuro miliyan 100 kafin Borussia Dortmund ta bar dan wasanta mai shekara 18, Jude Bellingham ya bar kungiyar, bayan da Manchester City da kuma Liverpool ke son daukar dan wasan. (Bild - in German)

West Ham, itama kamar Dortmund, ta yi wa fitaccen dan kwallonta farashi. The Hammers na neman fam miliyan 100 ga duk wanda ke son daukar dan kwallon tawagar Ingila, Declan Rice, mai shekara 22 daga kungiyar. (football.london)

Chelsea na shirin bai wa dan wasa mai shekara 22, Mason Mount sabuwar kwantiragi da zai ke karbar albashin da zai kai fam 150,000 a duk mako. (90min)

Dan kwallon Manchester United mai tsaron baya, Axel Tuanzebe, mai shekara 23 wanda ke wasa a aro a Aston Villa na son komawa kungiyar gabaki daya. (Sun)

Bayern Munich na duba hanyar da za ta sayo dan kwallon Chelsea dan kasar Jamus, Timo Werner, mai shekara 25, daga Chelsea a watan Janairu. (Football Insider)

Dan kwallon tawagar Faransa, Paul Pogba, mai shekara 28, wanda ake alakanta shi da zai koma ko dai Paris St-Germain ko kuma Real Madrid, zai saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da taka leda a Manchester United bayan da Christiano Ronaldo ya sake komawa Old Trafford. (Athletic, subscription required)

Leicester City na sha'awar daukar dan wasan Manchester United mai shekara 28 dan kwallon tawagar Ingila, Jesse Lingard. (Fichajes - in Spanish)

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Watakila Chelsea ta yi kokarin sayo masu tsaron bayan Inter Milan Alessandro Bastoni da kuma Milan Skriniar. (Mediaset - in Italian)

Tottenham ta ajiye kudin da za ta sayi dan wasan AC Milan farashi wato Franck Kessie, mai shekara 24, amma ba a da tabbaci ko za ta yi shirin daukar dan wasan Ivory Coast a watan Janairu ko za ta jira kwantiraginsa ta kare a kungiyar da ke buga Serie A. (Calciomercato, in Italian)

Tsohon dan wasan Bayern Munich Karl-Heinz Rummenigge, ya ce ba wata kungiya a Bundesliga da za ta iya sayen Erling Haaland, saboda farashi mai yawa da Borussia Dortmund za ta sa a kan dan kwallon. (AS, in Spanish)

Liverpool ta nuna sha'awar sayen dan kwallon Nice mai cin kwallo Amine Gouiri, bayan da Jurgen Klopp ke bibiyar wasannin dan kwallon tawagar Faransa mai shekara 21. (Fichajes, in Spanish)

Arsenal tana daga cikin kungiyoyinPremier League da ke son daukar dan wasan Sweden, Alexander Isak, mai shekara 21, duk da cewar dan kwallon Real Sociedad ya tsawaita yarjejeniyar ci gaba da taka leda a kaka biyar a kungiyar ta Sifaniya. (Fichajes via FourFourTwo)

Manchester United na tuntubar Barcelona ko za a sayar mata da matashin dan kwallon Sifaniya, Ansu Fati, mai shekara 18 ta hannun mai kula da wasannin Christiano Ronaldo, Jorge Mendes. (Mundo Deportivo, in Spanish)

Tottenham za ta iya sallamar dan kwallonta Harry Winks a karshen kakar bana ga duk wadda zai biya fam miliyan 40 kudin dan wasan mai shekara 25. (Times, subscription required)