Barcelona vs Bayern Munich: 'Yan Barca da za su karbi bakuncin Bayern a Camp Nou

Ronald Koeman

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ronald Koeman

Kocin Barcelona, Ronald Koeman ya bayyana 'yan wasa 23 da zai fuskanci Bayern Munich a gasar Champions League ranar Talata.

Bayern Munich za ta ziyarci Barcelona a wasa na farko na cikin rukuni na biyar a gasar zakarun Turai ta bana.

'Yan wasan Barcelona da za su kara da Bayern Munich:

Ter Stegen da Dest da Pique da R. Araujo da Sergio da Riqui Puig da Memphis da Demir da Neto da Coutinho da Lenglet da Pedri da kuma L. De Jong.

Sauran sun hada da Jordi Alba da S. Roberto da F. De Jong da O. Mingueza da Umtiti da Eric da Inaki Pena da Nico da Gavi da kuma Balde.

Barcelona za ta buga wasan Champions League da Bayern a karon farko ba Lionel Messi tun bayan da kyaftin din Argentina ya buga karawar da kungiyar Jamus ta yi nasara da ci 2-1 a Nuwambar 1998.

Messi ya koma taka leda a Paris St Germain a bana, bayan da Barcelona ta shiga matsin tattalin arziki da ya sa ta kasa tsawaita yarjejeniyar tsohon kyaftin dinta.

A kakar 2019/20 kungiyoyin biyu suka kara a wasan daf da na kusa da na karshe a Porugal, inda Bayern ta yi nasara da ci 8-2.