'Yan Real da za su kara da Mallorca a La Liga ran Laraba

Camavinga and Ancelotti

Asalin hoton, Getty Images

Real Mallorca ta ziyarci Real Madrid, domin buga wasan mako na shida a gasar La Liga ranar Laraba.

Tuni kocin Real Madrid, Carlo Ancelotti ya bayyana 'yan wasan da za su fuskanci Mallorca ciki har da matashi daga Castilla, Sergio Santos.

Real Madrid za ta karbi bakuncin Mallorca ba tare da dan wasa Dani Carvajal da Ferland Mendy da kuma Marcelo, inda ake sa ran Lucas Vazquez zai tsare baya daga hagu, yayin da matashi, Sergio Santos zai yi zaman ko-ta-kwana.

Wani matashin dan wasan Castilla, Miguel Gutierrez, wanda ya buga wa babbar kungiyar karawa biyu a bana, yana daga cikin wadanda za su fafatata a wasa.

Haka fitattun 'yan wasa da suka hada da Toni Kroos da Gareth Bale da kuma Dani Ceballos ba za su buga wasan ba, amma dai Mariano Diaz, wanda ya sha jinya yana daga cikin wadanda za su buga wa Real wasan mako na shida ranar Laraba.

'Yan wasan Real Madrid da za su fuskanci Mallorca:

Masu tsaron raga: Thibaut Courtois da Andriy Lunin da Toni Fuidias.

Masu tsaron baya: Eder Militao da David Alaba da Jesus Vallejo da Nacho Fernandez da Lucas Vazquez da Miguel Gutierrez da kuma Sergio Santos.

Masu wasa daga tsakiya: Luka Modric da Casemiro da Fede Valverde da Isco da Eduardo Camavinga da kuma Antonio Blanco.

Masu cin kwallye: Eden Hazard da Karim Benzema da Marco Asensio da Luka Jovi da, Vinicius Junior da Rodrygo Goes da kuma Mariano Diaz.