Kauwar 'yan kwallo: Martial daHenderson da Kante da Koeman da Oyarzabal da kumaAsensio

Anthony Martial

Asalin hoton, Getty Images

Dan kwallon tawagar Faransa, Anthony Martial zai iya barin Manchester United a watan Janairu idan an bude kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo ta Turai. Mai shekara 25 na son ci gaba da zama a Old Trafford, amma kila ya gwada kwazonsa a wata kungiyar watakila ma Barcelona. (Eurosport)

Dan wasan Manchester United mai tsaron ragar Ingila, Dean Henderson, mai shekara 24, na son a bayar da aronsa ga wata kungiya a watan Janairu. (Sun)

Chelsea na shirye-shiryen tsawaita kwantiragin 'yan wasa uku da ya hada da Mason Mount da N'Golo Kante, 30 da kuma Jorginho. (Standard)

Chelsea a shirye take ta taya dan kwallon Paris St-Germain dan Brazil Marquinhos, kan fam miliyan 86 a kaka mai zuwa. (RMC Sport - in French)

Manchester City na bibiyar wasannin dan kwallon Real Sociedad, Mikel Oyarzabal, mai shekara 24. (TeamTalk)

Arsenal za ta sa Bernd Leno a kasuwa, bayan da ta dauki matashin mai tsaron raga Aaron Ramsdale a bana. (Eurosport)

Barcelona na shirin raba gari da kocinta, Ronald Koeman, wanda Roberto Martinez ke shirin maye gurbinsa a kowanne lokaci nan gaba. (Goal)

Koda yake, shugaban Barcelona, Joan Laporta bai yanke tsammanin sake daukar kociyan Manchester City, Pep Guardiola zuwa Nou Camp. Guardiola, ya ja ragamar Barca ta lashe La Liga uku da Champions Leagues biyu a kaka hudun da ya yi tsakanin 2008 zuwa 2012. (El Nacional - in Spanish)

Watakila Marco Asensio, ya bar Real Madrid idan har baya samun buga wasanni sosai karkashin koci Carlo Ancelotti a bana. (Cadena Ser - in Spanish)

Ana shirin karawa Joao Palhinha albashi mai tsoka a Sporting Lisbon, bayan da ake alakanta shi da cewar zai koma taka leda a ko dai Everton ko Tottenham ko kuma Wolves. (A Bola - in Portuguese)

Mai tsaron ragar tawagar Kamru da Ajax, Andre Onana, ya yi farin jini, bayan da Inter Milan da kuma Napoli ke son yin zawarcin dan kwallon. (Calciomercato - in Italian)