Samuel Eto'o zai tsaya takarar shugaban hukumar kwallon kafar Kamaru

Samuel Eto'o

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Samuel Eto'o ya ci kwallo 56 a wasanni 118 a matsayin sa na dan wasan Kamaru

Tsohon dan wasan kwallon kafa na Kamaru Samuel Eto'o zai tsaya takarar shugabancin hukumar kwallon kafar Kamaru (Fecafoot).

Tsohon dan kwallon na Barcelona da Inter Milan ya sanar da hakan a shafukansa na sada zumunta a ranar Talata da yamma, yana cewa ya dauki matakin ne "saboda soyayyar da yake yi wa Kamaru da kwallon kafa."

"Lokaci yana kurewa. Ba za mu iya jira ba. Lokaci ya yi da za mu gina harkar kwallon kafarmu," in ji Eto'o.

Ana sa ran za a yi zaben hukumar kwallo ta Fecafoot ranar 11 ga Disamba, inda za a fara wasannin Gasar Kofin Afirka a Kamarun ranar 9 ga watan Janairun 2022.

Fecafoot ba ta sanar da cewa za ta saki jerin sunaye na karshe na 'yan takarar shugabancin hukumar.

Eto'o mai shekara 40, fitaccen dan wasa ne, inda ya sha yin nasara a gasanni na cikin gida da na Turai a Spaniya da Italiya.

Dan wasan wanda ya ci zaben dan kwallon Afirka da ya fi kowa sau hudu ya zura kwallo 56 a raga ya kuma ci wasanni 118 sannan ya yi zarra ma a gasar Firimiyar Ingila a Chelsea da Everton, inda ya kawo karshen aikinsa a Qatar.

A matakin wasanni na duniya kuwa, ya taimaka wa Kamaru ta ci Gasar Kofin Afirka a 2000 da 2002 sannan ya ciyo kambun zinare a Gasar Olympic ta Sydney 2000.

Sanarwar ta Eto'o ta zo ne a lokacin da ake tsaka da ce-ce-ku-ce a Kamaru bayan da aka ce wa 'yan takara masu shaidar kasa biyu ba za su iya tsayawa takara a zaben ba. An taba bai wa Eto'o takardar shaidar zama dan kasa a Spaniya a lokacin da ayke yi wa Barcelona wasa.

Zuwa yanzu dai Eto'o ne mutum na uku daga cikin tsofaffin 'yan wasan Kamaru da zai tsaya takarar shugabancin hukumar kwallon kafar.

Jules Denis Onana da Emmanuel Maboang Kessack, wadanda dukkaninsu sun buga wa Kamaru wasa a Gasar Cin Kofin Duniya ta 1990, su ma suna takarar.

'Yan takara na da lokaci har zuwa 11 ga watan Oktoba don su bayyana aniyarsu ta tsayawa.