James Rodriguez: Dan wasan Everton ya koma Qatari a kungiyar Al Rayyan

James Rodriguez

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

James Rodriguez ya saka hannu kan yarjejeniyar komawa Everton cikin watan Satumbar 2020

Dan kasar Colombia, James Rodriguez ya kammala komawa kungiyar Al Rayyan ta Qatar daga Everton, amma ba a fayyace kudin cinikinsa ba.

Mai shekara 30 da haihuwa, ya bar Goodison Park, bayan wata 12 da ya koma Everton da taka leda.

Wanda ya koma taka leda Ingila daga Real Madrid ya ci kwallo shida a dukkan fafatawa 26 da ya yi wa Evrton.

Sai dai kawo yanzu sabon koci Raphael Benitez bai saka Rodriguez a wasannin Everton ba.

Wasan karshe da ya buga wa kungiyar tun ranar 16 ga watan Mayu a wasan da Sheffield United ta ci Everton 1-0.