Arsenal 3-0 AFC Wimbledon: Arsenal ta yi waje da Wimbledon a Carabao Cup

Eddie Nketiah

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Eddie Nketiah ya buga wa Arsenal wasan farko a bana da cin kwallo na uku a wasan

Arsenal ta doke mai buga gasar League One AFC Wimbledon ta kuma kai zagaye na hudu a gasar Carabao Cup.

Da wannan sakamakon Gunners ta ci wasa na uku a jere a bana, har da biyun da ta ci a Premier League, wato wanda ta doke Norwich City da kuma Burnley.

Alexandre Lacazette wanda ya fara buga wa Gunners kwallo a bana a karon farko tun bayan watan Afirilu ya ci kwallo a bugun fenariti, bayan da Nesta Guinness-Walker ya yi wa Gabriel Martinelli keta.

Daga nan kuma Gunners ta kara na biyu ta hannun Emile Smith Rowe, bayan da ya samu kwallo daga wajen Lacazette.

Arsenal ta ci na uku ta hannun Eddie Nketiah kuma mai kayatarwa da hakan ya tabbatar da fitar da Wimbledon daga gasar bana.

Ya ci a ce Gunners ta zura kwallaye da yawa a raga, bayan da ta buga kwallo ya bugi turke har sau biyu.

Gunners ta buga karawar da fitattun 'yan wasanta, inda Nketiah ne kadai bai yi karawar Premier League ba a kakar nan.

AFC Wimbledon ba ta buga kwallo koda daya ya nufin ragar Arsenal ba a fafatawar.