Jadawalin Carabao Cup zagaye na hudu: Manchester City da West Ham, Arsenal da Leeds

Manchester City celebrate against West Ham

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Manchester City are unbeaten in their last 12 games with West Ham

Mai rike da kofin Carabao, Manchester City za ta ziyarci West Ham United a wasan zagaye na hudu a gasar bana.

West Ham ta kai matakin gaba, bayan da ta ci Manchester United 1-0 ranar Laraba, za ta karbi bakuncin Manchester City a karawar zagayen gaba.

Kungiyar da ke buga gasar Championship, Preston za ta karbi bakuncin Liverpool a Deepdale, yayin da Arsenal za ta kece raini da Leeds, ita kuwa Chelsea za ta karbi bakuncin Southampton a Stamford Bridge karawar masu buga Premier League kenan.

Ita kuwa Sunderland wadda ita kadai ta rage mai buga gasar League One za ta ziyarci QPR mai yin wasannin Championship.

Za a buga wasannin ranar 25 ga watan Oktoba,

Jadawalin wasannin zagaye na hudu a Carabao Cup

  • Chelsea da Southampton
  • Arsenal da Leeds
  • Stoke da Brentford
  • West Ham da Manchester City
  • Leicester da Brighton
  • Burnley da Tottenham
  • QPR da Sunderland
  • Preston da Liverpool