Tawagar Argentina ta gayyaci Lionel Messi da Angel Di Maria

Lionel Messi and Angel Di Maria celebrate after Argentina beat Switzerland

Asalin hoton, Getty Images

Hukumar kwallon kafa ta Argentina ta bai wa 'yan wasan Paris St Germain uku goron gayyata, domin buga mata gasar a cin kofin duniya cikin watan Nuwamba.

Cikin 'yan wasan da ta gayyata daga PSG sun hada da kyaftin Lionel Messi da Angel Di Maria da Leandro Paredes.

Argentina karkashin koci, Lionel Scaloni za ta buga wasa biyu a shiyyar Kudancin Amurka, domin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a Qatar a 2022.

Ranar Asabar 13 ga watan Nuwamba, Argentina za ta ziyarci Uruguay da za su fafata a Campeon del Siglo, Montevideo.

A kuma ranar Laraba 17 ga Nuwamba Argentina za ta karbi bakuncin Brazil a wasan hamayya da za su kara a Estadio del Bicentenario, San Juan.

Brazil ce ta daya a rukunin Kudancin Amurka da maki 31, sai Argentina ta biyu da maki 25 da kuma Ecuador mai maki 17 ta uku a kan teburi.