Za a raba jadawalin zagaye na biyu a Champions League ranar Litinin

Chelsea FC

Asalin hoton, Getty Images

Ranar Litinin za a raba jadawalin zagaye na biyu a Champions League da za a yi a hedikwatar UEFA a Nyon a Switzerland.

Abin da ya kamat ku sani kan raga jadawalin Champions League:

Kawo yanzu kungiyoyi 15 ne suka kai wasannin zagaye na biyu a Champions League da za a raba jadawalin ranar Litinin, ana jiran wadda za ta zama ta 16 tsakanin Atalanta da Villarael da aka soke wasansu suna 2-2.

Tuni UEFA ta tsara cewar duk wadanda suka ja ragamar rukuni sune za su kai ziyara a wasannin farko. Chelsea ce ke rike da kofin bara da ta lashe, bayan doke Manchester City.

Wadanda suka ja ragamar kowanne rukuni

  • Ajax daga Netherlands
  • Bayern Munich daga Jamus
  • Juventus daga Italiya
  • Liverpool daga Ingila
  • Lille daga Faransa
  • Manchester City daga Ingila
  • Manchester United daga Ingila
  • Real Madrid daga Sifaniya

Wadanda suka yi na biyu a cikin rukuni

  • Atletico Madarid daga Sifaniya
  • Benfica daga Portugal
  • Chelsea daga Ingila
  • Inter Milan daga Italiya
  • Paris Saint-Germain daga Faransa
  • Salzburg daga Australiya
  • Sporting daga Portugal
  • Sauran daya da ake jira tsakanin Atalanta da Villareal

Asalin hoton, Getty Images

Ko kungiyoyin da take kasa zasu iya haduwa a tsakaninsa a zaganen kungiyoyi 16 a Champions League kuwa?

Ba kungiyar da za ta kara da wadda suka fita daga kasa daya a zagaye na biyu a gasar, sannan wadanda suka hadu a cikin rukuni ba za su sake fafatawa ba a zagaye na biyu ba.

Ko zagaye na biyun za a yi wasannin gida da waje ne?

Za a buga wasannin zagaye na biyu gida da waje, sannan wadanda suka yi na daya a kowanne rukuni ne za su karbi bakuncin fafatawa ta biyu a gida kenan.

Asalin hoton, Reuters

Yaushe za a fara karawar zagaye na biyu a Champions League?

Za a fara wasan farko tsakanin 15/16/22/23 ga watan Fabrairu February, yayin da za a yi fafatawa ta biyu tsakanin 8/9/15/16 ga watan Maris.

Za kuma a raba jadawalin wasan daf da na kusa da na karshe da na daf da karshe ranar Juma'a 18 ga watan Maris.

Wane sauyi aka samu a Champions League?

An sauya amfana da cin kwallaye da ake cewa away goals, yanzu idan aka yi minti 180 ba ci, sai a kara lokaci idan ba wadda ta ci sai a yi bugun daga kai sai mai tsaron raga.