Da kyar da gumin goshi Manchester United ta doke Norwich City

Cristiano Ronaldo

Asalin hoton, Getty Images

Manchester United ta doke Norwich City da kyar da gumin goshi a wasan mako na 16 a gasar Premier League ranar Asabar.

United ta yi nasara ne da ci 1-0 a fafatawar da suka yi a Old Trafford, inda Cristiano Ronaldo ne ya ci kwallon a bugun fenariti.

Kwallon da Ronaldo ya ci shine na shida da aka zura a raga a bugun fenariti a wasannin mako na 16 da aka buga a babbar gasar Ingila, an taba yin bakwai a rana daya wato ranar 5 ga watan Fabrairun 2011.

Haka kuma Ronaldo ya zama na uku da ya zura kwallo karkashin koci uku a Manchester United wato a lokacin Ole Gunnar Solskjaer da Michael Carrick da kuma Ralph Rangnick a kaka daya, bayan James Hanson da kuma Joe Spence da suka yi a 1926-27 (masu haorar wa Chapman da Hilditch da kuma Bamlett).

Haka kuma sabon kocin rikon kwarya, Ralf Rangnick ya zama na biyu a Manchester United da fara cin wasa biyu a jere ba tare da kwallo ya shiga raga ba, bayan bajintar da Ernest Mangnall ya yi a 1903.

Jerin Fenariti 6 da aka ci ranar Asabar a gasar Premier League:

  • Raheem Sterling ya ci wa Manchester City fenaritin da ta yi nasara a kan Wolverhampton a Etihad.
  • Raphinha ne ya fara cin Chelsea a bugun daga kai sai mai tsaron raga a minti na 22 da Leeds ta ziyarci Stamford Bridge.
  • Sai guda biyu da Jorginho ya ci Leeds a bugun fenariti a minti na 58 da kuma a minti na 90.
  • Haka shima Mohamed Salah ya ci Aston Villa a bugun fenariti ranar Asabar, kuma kwallo na 14 da ya ci a kakar bana.
  • Sai kuma wadda Cristiano Ronaldo ya zura a ragar Norwich City a bugun daga kai sai mai tsaron raga a Old Trafford.

Asalin hoton, Getty Images

Golan Manchester United, David de Gea ya taka rawar gani domin ya hana Norwich City ta zura masa kwallo a raga.

Kuma kungiyar ta Carrow Road ta sawa United masti tun farko fara wasa har zuwa aka kammala, ta kuma samu damar da yawa da golan United ya sa kwazo.

Da wannan sakamakon United tana ta biyar a kan teburin Premier da maki 27, ita kuwa Norwich City tana ta karshe mai maki 10.