Osasuna 2-2 Barcelona: Xavi ya kara yin tuntube a gidan Osasuna

Asalin hoton, Getty Images
Barcelona ta je ta tashi 2-2 a gidan Osasuna a wasan mako na 17 da suka kara a gasar La Liga ranar Lahadi.
Barcelona ce ta fara cin kwallo ta hannun Nico Gonzalez minti 12 da fara tamaula daga baya Osasuna ta farke ta hannun David Garcia minti biyu tsakani.
Barcelona ta kara na biyu bayan minti hudu da suka koma daga hutu ta hannun Abde Ezzalzouli, saura minti uku a tashi daga fafatawar Osasuna ta farke ta hannun Ezequiel Avila.
Xavi wanda ya karbi aikin horar da Barcelona cikin watan Nuwamba, bayan maye gurbin Ronald Koeman ya ja ragamar wasa shida da yin nasara biyu da canjaras biyu da shan kashi a fafatawa biyu.
Tun kan wasan na ranar Lahadi, Barcelona ta yi rashin nasara a hannun Real Betis da ci 1-0 a Camp Nou a gasar La Liga ranar 4 ga watan Disamba, sannan kwana hudu tsakani Barcelona ta yi ban kwana da gasar Champions League, bayan da Bayern Munich ta doke ta 3-0 a Jamus.
Kenan Bayern Munich ta yi nasara a kan kungiyar Camp Nou gida da waje da cin kwallo 6-0.
Barcelona za ta buga Europa League da za a fara cikin watan Fabrairu, bayan da ake sa ran raba jadawali ranar Litinin.