NFF ta kori Rohr, ta nada Eguavoen kocin riko a Super Eagles

Asalin hoton, The NFF
Hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF ta sanar da korar kocin Super Eagles Gernat Rohr, kuma a lokaci guda ta bada sanarwar nada Augustine Eguavoen a matsayin kocin rikon kwarya domin ya ja ragamar Super Eagles.
NFF ta Gernot Rohr, wanda ke kan aiki wata 64 a matakin kociyan Najeriya da ya dade a kan mukamin.
NFF ta sanar a shafinta na intanet cewar Eguavoen zai yi aiki tare da Salisu Yusuf da Paul Aigbogun da Joseph Yobo da Dr Terry Eguaoje, yayin da Aloysius Agu zai horar da masu tsaron raga.
An kuma nada tsohon kyaftin din Super Eagles, Augustine 'Jay Jay' Okocha da Nwankwo Kanu da kuma Garba Lawal da za su taimaka musu da kuma aikin jakada.
Magatakardan NFF, Dakta Mohammed Sanusi ya kara da cewa: ''An kawo karshen yarjejeniya tsakanin hukumar kwallon kafa ta Najeriya da Genor Rohr. Mun gode kan aiki jan ragamar Super Eagles da ya yi.''
''Muna kuma mika godiya ga ma'aikatar matasa da wasanni ta kasa kan rawar da ta take takawa da bayar da shawarwari.''
Eguavoen tsohon kyaftin din Najeriya ya yi kocin tawagar a gasar cin kofin nahiyar Afirka a Masar a 2006 da Super Eagles ta yi ta uku.
Haka kuma shine kyaftin din tawagar da ya daga kofin nahiyar Afirka a Tunisia shekara 27 da ta wuce da Super Eagles ta zama zakara.
Yanzu shine zai horar da Najeriya a shirye shiryen da take na halartar gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a yi a Kamaru, tsakanin 9 ga watan Janairu zuwa 6 ga watan Fabrairun 2022 kafin a nada sabon koci.