Sergio Aguero: Dan wasan Barcelona zai sanar da ya yi ritaya ranar Laraba

Asalin hoton, Getty Images
Rabon da Sergio Aguero ya taka leda a Barcelona tun cikin Oktoba, wadda ya yi wa karawa biyar
Sergio Aguero na shirin sanar da yin ritaya ranar Laraba kasa da wata shida, bayan da ya koma Barcelona in ji rahoton Guillem Balague.
Mai shekara 33 na fama da jinya da rashin lafiya, tun bayan da ya koma Sifaniya da taka leda, wanda ya buga wa Barcelona wasa biyar.
A karawar karshe da ya buga ranar 30 ga watan Oktoba an sauya shi a fafatawar, bayan da kirjinsa ya kama yi masa ciwo.
Aguero ya kammala sana'arsa ta tamaula da cin kwallo 427 a wasa 786 da ya yi.
Zakakurin dan wasan Premier League
Bayan da ya fara taka leda a Independiente ta Argentina, ya koma Atletico Madrid, inda ya lashe Europa League a 2010 da cin kwallo 101 a wasa 234.
Daga nan ya koma Manchester City ta dauke shi kan fam miliyan 38, wanda ya zama gwarzo a Etihad da gasar Premier League da ya yi kaka 10 a Ingila.
Aguero ya koma Camp Nou, bayan cin kwallo 260 a wasa 390 har da cin kwallo uku rigis sau 16.
Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus
Kashi-kashi
End of Podcast
Shine dan wasa daga waje da ya ci kwallaye da yawa a gasar Premier League mai 184 a raga da tazarar tara tsakaninsa da tsohon dan wasan Arsenal, Thierry Henry.
Wadanda suka zazzaga kwallaye a raga a Premier League sun hada da Alan Shearer mai 260 da Wayne Rooney mai 208 da kuma Andrew Cole da ya ci 187 a raga.
Ya kuma lashe Premier League biyar da FA Cup da League Cups shida a wasannin tamaula da ya yi a Ingila.
Barcelona ba za ta mori Aguero ba
Abota da ke tsakanin Aguero Lionel Messi ta sa ya koma taka leda a Barcelona, bayan da Manchester City ta amince ya bar Etihad a karshen kakar nan.
Sai dai kuma ya koma Camp Nou a lokacin da Barcelona ke fuskantar kalubale matsin tattalin arziki da kasa sayen fitattun 'yan wasa har da ta kai Messi ya koma wasa a Paris St-Germain.
Bayan da Aguero ya kulla yarjejeniya da Barcelona sai kuma ya ji raunin da ya jinya har zuwa watan Oktoba.
Shine ya ci kwallo daf da za a tashi a wasan El Clasico da Real Madrid ta yi nasara ranar 24 ga watan Oktoba, wasan da ya fara yi mata.
Ranar 330 ga watan Oktoba ya buga wasa da Alaves, amma sai sauya shi aka yi, bayan ciwon kirji, inda Aguero ya sanar a shafinsa na sada zumunta cewar zai bi shawarar da likitoci suka gindaya masa kan makomar wasanninsa na tamaula.
Shawarar da likitoci suka bashi ce zai tabbatarwa duniya a ranar Laraba.
Wasan karshe da ya buga wa Argentina shine a gasar Copa America karawar daf da na kusa da na karshe da Ecuador, wanda Argentina ta lashe kofin a karon farko, bayan shekara 28.