Barcelona za ta kara da Napoli a Europa League

Asalin hoton, UEFA
Kungiyar Barcelona za ta fafata da Napoli a wasan zagaye na biyu a gasar zakarun Turai ta Europa League.
A jadawalin da UEFA ta gudanar a Switzerland ranar Litinin, an hada karawa tsakanin Borussia Dortmund da Rangers.
Barcelona ta kasa kai wa karawar zagaye na biyu a Champions League, shi ya sa za ta koma buga Europa League a karon farko tun bayan kakar 2003-04.
Tun daga lokacin kungiyar ta Camp Nou ta lashe Champions League hudu daga biyar da ta buga, sai dai a bana ta kasa zuwa zagaye na biyu, bayan da Bayern Munich ta doke ta 3-0 a makon jiya da hakan ya sa za ta buga Europa League kenan.
Kofin Europa League shine kadai da Barca ba ta daga ba, ita kuwa Napoli ta dauki kofin a 1989 a lokacin da Diego Maradona ya yi mata wasa.
A baya a Champions League wasan zagaye na biyu, Barcelona ce ta yi nasara kai wa matakin gaba da cin kwallo 4-2 daga nan ne Bayern Munich ta casa Barcelona 8-2 a wasan daf da na kusa da na karshe da suka yi karawa daya don gudun yada cutar korona.
Jadawalin kungiyoyi 16 da za su buga karawar zagaye na biyu a Europa League:
- Sevilla da Dinamo Zagreb
- Atalanta da Olympiacos
- Leipzig da Real Sociedad
- Barcelona da Napoli
- Zenit da Betis
- Dortmund da Rangers
- Sheriff da Braga
- Porto da Lazio
Za a buga wasan farko ranar 17 ga watan Fabrairu, sannan a yi wasa na biyu mako daya tsakani.
Villareal ce ke rike da kofin wadda ke buga Champions League a bana.