Arsenal: An karbe kyaftin daga hannun Pierre-Emerick Aubameyang

Asalin hoton, EPA
Aubameyang ya karbi kyaftin din Arsenal daga Granit Xhaka
Arsenal ta karbe mukamin kyaftin daga hannun Pierre-Emerick Aubameyang sakamakon nuna halin rashin da'a.
Dan kwallon tawagar Gabon, wanda bai buga wasan da Arsenal ta doke Southampton 3-0 ranar Asabar a gasar Premier League ba, ba zai kuma yi wa Gunners fafatawar da za ta kara da West Ham ba ranar Laraba a babbar gasar Ingila.
"Muna sa ran dukkan 'yan wasanmu, musamman kyaftin dinmu da zama mai bin dokokin da muka gindaya da aka amince da su'' in ji wani rahoto da Arsenal ta fito.
An taba ajiye Aubameyang mai shekara 32 awanni kan wasan Arsenal a cikin watan Maris - shine karawar da Gunners ta doke Tottenham kan halin rashin da'a.
Koda yake Mikel Arteta bai fayyace laifin da dan kwallon Gabon ya aikata ba, sai dai Athletic ta bayar da rahoton cewar dan wasan ya koma latti, bayan wata tafiya da ya yi ba bisa izini ba.
Aubameyang ya karbi mukamin kyaftin a Nuwambar 2019 a hannun Granit Xhaka karkashin koci Unai Emery.
Aubameyang, wanda ya koma Arsenal kan fam miliyan 56 daga Borussia Dortmund a 2018, ya saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da taka leda kaka uku a Emirates a bara.
A kakar tamaula ta bana ya ci kwallo hudu a wasa 14 a lik, sai dai rabon da ya zura kwallo a raga tun ranar 22 ga watan Oktoba.
Arsenal tana mataki na shida a teburin Premier League da tazarar maki 12 tsakaninta da Manchester City mai jan ragama.