Champions League: Sau nawa PSG da Real Madrid suka kara

Benzema Neymar

Asalin hoton, Getty Images

Paris St Germain za ta fafata da Real Madrid a wasan zagaye na biyu a Champions League, bayan da aka raba jadawali ranar Litinin.

Za su fara bugan wasan farko a tsakaninsu a birnin Paris ranar 15 ga watan Fabrairu, sannan karawa ta biyu a yi a Santiago Bernabeu ranar 9 ga watan Maris.

Kungiyar Faransa ta kai zagaye na biyu a wasannin kungiyoyi 16, bayan da ta yi ta biyu a rukunin farko da Manchester City ta yi ta daya.

PSG wadda ta kai karawar daf da karshe a bara ta ci wasa uku dukka a gida da canjaras biyu da rashin nasara a fafatawa daya da ta hada maki 11 a cikin rukunin farko.

Messi ya ci kwallo hudu iri daya da wadda Mbappe ya zura a raga a Champions League a bana.

Real Madrid ta ci wasa biyar da rashin nasara a karawa daya da hada maki 15 a rukunin na hudu - Karim Benzema na Real Madrid yana da kwallo biyar a raga.

Tun farko an hada jadawalin ne tsakanin Real Madrid da Benfica a safiyar Litinin, daga baya UEFA ta fuskanci ta yi kuskure, bayan da na'ura ta yi tustsu ta hada Manchester United da Villareal, wadanda suka hadu a wasannin rukuni.

A dokar UEFA kungiyoyin da suka hadu a cikin rukuni da wadanda suka fito daga kasa daya ba za su hadu a karawar zagaye na biyu ba.

An kara tsakanin PSG da Real Madrid sau shida, inda Real ta yi nasara a wasa uku da canjaras biyu, inda kungiyar Faransa ta yi nasara daya.

Fafatawar da aka yi tsakanin PSG da Real Madrid:

Kakar 2019/2020

Champions League ranar Talata 26 ga watan Nuwambar 2019

 • Real Madrid 2 - 2 Paris St-Germain

Champions League ranar Laraba 18 ga watan Satumbar 2019

 • Paris St-Germain 3 - 0 Real Madrid

Kakar 2017/2018

Champions League ranar Talata 6 ga watan Maris 2018

 • Paris St-Germain 1 - 2 Real Madrid

Champions League ranar Laraba 14 ga watan Fabrairun 2018

 • Real Madrid 3 - 1 Paris St-Germain

Kakar 2015/2016

Champions League ranar Talata 3 ga watan Nuwambar 2015

 • Real Madrid 1 - 0 Paris St-Germain

Champions League ranar Laraba 21 ga watan Oktobar 2015

 • Paris St-Germain 0 - 0 Real Madrid

Yadda aka raba jadawalin Champions League:

 • Salzburg da Bayern Munich
 • Sporting da Manchester City
 • Benfica da Ajax
 • Chelsea da Lille
 • Atletico da Manchester United
 • Villarreal da Juventus
 • Inter da Liverpool
 • PSG da Real Madrid