Maradona Cup: Barcelona da Boca Juniors a Saudi Arabia

Diego Maradona

Asalin hoton, Getty Images

Barcelona za ta fafata da Boca Juniors a wasan tunawa da Diego Maradona ranar Talata a Saudi Arabia.

Tsohon kyaftin din tawagar kwallon kafar Argentina ya mutu ranar 25 ga watan Nuwambar 2020.

Maradona ya buga wa kungiyoyin biyu tamaula karo biyu a Boca Juniors tsakanin 1981/82 daga nan ya koma Barcelona har zuwa lokacin da ya yi ritaya a 1995 zuwa 97.

Za su kara ne a tsakaninsu a Saudi Arabia a yammacin Talata.

Karawa tsakanin kungiyoyin biyu:

Barcelona da Boca Juniors sun kara sau 10 a wasannin sada zumunta har da shida a gasar Joan Gamper Trophy.

Wasan karshe da suka fafata shine a 2018 a gasar Joan Gamper Trophy, inda Barcelona ta yi nasara da ci 3-0, wadanda suka ci mata kwallayen Malcom da Leo Messi da kuma Rafinha.

Wasa a Saudi Arabia:

Wannan shine karo na biyu da Barcelona za ta buga tamaula a Saudi Arabia, bayan Janairun 2020 da ta yi rashin nasara a hannun Atletico Madrid da ci 3-2 a daf da karshe a Spanish Super Cup.

Barcelona wadda ke rike da Copa del Rey za ta sake komawa Saudi Arabia buga wasa a karo na uku cikin watan Janairu, don fafatawa tsakaninta da Real Madrid da Athletic Club da kuma Atletico Madrid.

Labari kan kungiyoyin biyu:

Xavi Hernandez ya je Saudi Arabia da 'yan wasa 28 don fuskantar Boca Juniors.

Dani Alves, wanda ba zai buga wa Barcelona lik ba har sai watan Janairu, zai iya buga wannan wasan na sada zumunta.

Boca Juniors:

Kungiyar itace kan gaba a lashe kofuna a gasar Argentina mai 71 a tarihi ciki har da 34 Primera da 14 a kofunan cikin gida.

Sun kuma lashe Copa Libertadores na Kudancin Amurka karo shida, kofin da yake da daraja irin ta Champions League, kuma ita ce ta biyu a yawan lashewa, bayan takwararta daga Argentina Independiente mai bakwai a tarihi.