Sam Allardyce ya zama kocin Ingila

Sam Allardyce Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Sam Allardyce ya rike kungiyoyi da dama a Ingila

An nada Sam Allardyce a matsayin sabon kocin tawagar kwallon kafa ta Ingila.

Kocin mai shekaru 61 ya sanya hannu a kan kwantiragin shekara biyu bayan da aka amince kan kudin fansar da za a biya kungiyarsa ta Sunderland.

A bara ya taimakawa kulob din wurin samun damar cigaba da zama a gasar Premier.

Ya maye gurbin Roy Hodgson, wanda ya yi murabus bayan da aka fitar da Ingila a zagaye na biyu na gasar Euro 2016.

Wasan Allardyce na farko shi ne karawar da kasar za ta yi da Slovakia a ranar 4 ga Satumba na share fagen shiga Gasar cin Kofin Duniya ta 2018.

A yanzu Sunderland za su fara zawarcin wanda zai zamo kocin kulob din a karo na tara a cikin shekara takwas.

Labarai masu alaka