Carles Puyol ya shiga tsaka mai wuya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Carles Puyol ya sha suka saboda ya ce shi dan Spaniya ne

Tsohon dan kwallon Barcelona, Carles Puyol, ya sha suka bayan da ya furta cewar shi dan Spaniya ne a wata talla a talabijin.

A lokacin da aka kaddamar da wata talla da kamfanin Tencent Sports ya yi a intanet, dan wasan ya ce, “Ni ne Carles Puyol kuma ni dan Spaniya ne.''

Hakan ne ya harzuka ‘yan yankin Catalonia wurin da dan wasan ya fito da cewar ya ci mutuncinsu, bayan ya san suna fafutukar neman cin gashin kai.

Duk da Puyol ya buga wa Spaniya gasar cin kofin duniya da ta lashe a shekarar 2010 a Afirka ta Kudu, bai hana ‘yan yankin nasa mayar masa da martani na batanci a kafar sada zumunta ta Intanet ba.

A kokarin da ya yi na kare kansa, dan kwallon ya ce yana tallata gasar La Liga wanda shi jakada ne ga al’umar China, wadanda ba su san siyasar da ke tsakanin Spaniya da Catalan ba.

Puyol ya buga wa Barcelona wasanni 593, wanda ya yi ritaya a shekarar 2014, ya kuma buga wa Spaniya tamaula sau 100, ya kuma yi wa Catalonia wasanni shida duk da ba a ‘yantar da ita ba daga Spaniyar.

Labarai masu alaka