Mai Takwasara ya doke Nuran Dogon Sani

Image caption Ana cigaba da dambe bayan gasar mota

Bayan da aka kammala gasar motar hawa a jihar Kano, an ci gaba da yin damben gargajiya kamar yadda aka saba.

Tun da yammacin Laraba filin wasa na Ado Bayero Square da ke Sabon Gari Kano ya cika da 'yan kallio domin su kashe kwarkwatar ido.

A dambatawar da aka yi tsakanin Dan Hausa daga Kudu da Shagon Audu Tufak daga Arewa babu kisa a turmi ukun da suka kara.

Shi kuwa Habu Bahago Guramada buge Shagon Sarka daga Kudu ya yi a turmin farko, 'yan wasan biyu sun fafata a gasar mota , inda Habu ya yi nasara ya kuma kai wasan gaba.

Mai Takwasara kuwa daga bangaren Guramada doke Nuran Dogon Sani daga Arewa ya yi a turmi na biyu.

Dan Sama'ila daga bangaren Kudu a turmin farko ya samu nasarar kai Cikan Guranada kasa a gumurzun da suka yi.

Za a cigaba da gudanar da wasannin Damben gargajiyar da yammacin Alhamis.

Labarai masu alaka