Liverpool ta sallama tayin da aka yi wa Allen

Joe Allen Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Allen na cikin 'yan wasan da su ka wakilci Wales a Euro 2016

Liverpool ta amince da tayin da Stoke City ta yi wa Joe Allen, dan wasan tawagar Wales, kan kudi fan miliyan 13.

Kafar yada labarai ta Press Association (AP) ta ce Liverpool ta yi na’am da Stoke ta taya dan kwallon, wanda saura shekara daya yarjejeniyarsa ta kare a Anfield.

Ita ma tsohuwar kungiyarsa Swansea tana son ta maida shi can ya ci gaba da wasanninsa, wacce ya bari ya koma Liverpool a shekarar 2012.

Wasanni takwas Allen ya buga wa Liverpool a kakar da aka kammala, kuma tawagar Wales ta gayyace shi gasar kofin nahiyar Turai da aka yi a Faransa.

Labarai masu alaka