Kocin Ingila: Mourinho ya amince da Allardyce

Sam Allardyce Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Ranar Alhamis za a sanar da nadin Sam Allardyce

Kociyan Manchester United, Jose Mourinho, ya ce Sam Allardyce ne yafi dacewa a bai wa aikin horar da tawagar kwallon kafar Ingila.

Mourinho ya ce kociyan na Sunderland a shirye yake, ya kware wajen karfafa gwiwar ‘yan wasa, zai kuma dawo da karsashin tawagar.

Tsohon kociyan Ingila, Sven-Goran Eriksson, ya shaida wa BBC cewar kasancewar Allardyce ya dade yana jagorantar kungiyoyin gasar Ingila, yana da kwarewar da zai taka rawar gani.

Sai dai kuma Eriksson ya yi gargadin cewar ita nasara ba a samunta a sauwake cikin gaggawa, sai an yi hakuri.

A ranar Alhamis ake sa ran hukumar kwallon kafa ta Ingila za ta sanar da nada Sam Allardyce a matsayin wanda zai maye gurbin Roy Hodgson.

Labarai masu alaka