David Moyes ya zama kocin Sunderland

David Moyes Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption David Moyes ya maye gurbin Sam Allardyce

Sunderland ta nada David Moyes a matsayin sabon mai horas da 'yan wasan kungiyar kan yarjejeniyar shekara hudu.

Tsohon kocin na Everton da Manchester United, mai shekaru 53, zai maye gurbin Sam Allardyce wanda ya karbi jagorancin tawagar Ingila.

Ya ce "Na karbi ragamar wani babban kulob a Birtaniya, wanda ke da magoya baya, kuma ina azamar ganin na sake komawa fagen daga a gasar Premier."

Kocin wanda ya fito daga yankin Scotland, ya kasance yana zaman kashe-wando tun bayan da kulob din Real Sociedad na Spaniya ya salleme shi a watan Nuwamba.

A ranar Juma'a ne aka tabbatar da nadin Allardyce a matsayin wanda ya maye gurbin Roy Hodgson.

Labarai masu alaka