Song na shirin dawo da tagomashinsa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Song ya koma Barcelona kan yarjejeniyar shekara biyar daga Arsenal a 2012

Tsohon dan kwallon tawagar Kamaru, Alex Song, na fatan ya dawo kan ganiyarsa a wasan tamaula, bayan da ya koma Rubin Kazan ta Rasha aro daga Barcelona.

Dan wasan mai shekara 23, ya yi wasannin aro a West Ham United na tsawon kakar wasa biyu, inda ya buga mata tamaula sau 46.

Song ya koma Barcelona da murza-leda a shekarar 2012 daga Arsenal kan kudi fan miliyan 15, ya kuma buga wa Barca wasanni 65.

Rabon da Song ya yi wa Kamaru wasa tun bayan da aka kore shi a gasar cin kofin duniya ta 2014 a karawar da suka yi da Croatia.

Dan kwallon ya sanar da yin murabus daga buga wa Kamaru tamaula, bayan da aka ki mika masa goron gayyata zuwa gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 2015.

Labarai masu alaka