Hull City za ta buga tamaula a Kenya

Hakkin mallakar hoto Hull City
Image caption A cikin watan Agusta za a fara wasannin gasar Premier.

Hull City za ta zama kungiyar kwallon kafa ta Premier da za ta fara buga kwallon kafa a Kenya.

Hull za ta buga wasan sada zumunta da kwararrun 'yan wasan kasar ta Kenya a wani bangare na talla da ta kulla da SportPesa.

Babban jami'in kamfanin caca na SportPesa, Ronald Karauri, ya ce wasan zai zama share fage a kokarin da suke yi na tallata ayyukan da suke yi a gasar kofin duniya da za a yi a 2022.

Hull City ta kulla yarjejeniya mai tsoka ta shekara uku da kamfanin na Kenya mai yin caca ta yanar gizo.

Labarai masu alaka