Dan wasan Nigeria Akinyemi yana tsaka mai wuya

Image caption A cikin watan Agusta za a fara wasannin Olympic a Brazil

Dan wasan kwale-kwale na Najeriya Johny Akinyemi ya shaida wa BBC cewa ya shiga tsaka mai wuya a filin jirgin saman Frankfurt da ke Jamus a kan hanyarsa ta zuwa birnin Rio domin shiga gasar Olympics.

Ya kara da cewa bai san lokacin da zai karasa Rio de Janeiro, inda za a fara gasar ta Olympics ranar biyar ga watan Agusta.

A ranar Lahadi ne aka samu jinkiri a tashin jirgin da zai kai shi Rio daga birnin Manchester na kasar Ingilia.

Labarai masu alaka