Konta ta doke Venus a gasar kwallon tennis

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Karon farko kenan da Konta ta lashe babbar gasar tennis

'Yar Birtaniya, Johanna Konta, ta doke Venus Williams, ta kuma lashe babbar gasar wasan tennis a karon farko a Stanford.

Konta, mai shekara 25, ta samu nasara ne da ci 7-5 5-7 6-2 a karawar da suka yi a California, hakan ya sa ta bi sahun Heater Watson, wadda ta taba lashe gasar a shekarar 2016.

A baya can 'yar Birtaniya Sue Barker ta taba lashe gasar da aka yi a Stanford, bayan da ta doke Virginia Wade a 1977.

Labarai masu alaka