An soke wasa tsakanin Man Utd da Man City

Hakkin mallakar hoto All Sport

An soke wasan sada zumuntar da aka shirya yi tsakanin Manchester United da Manchester City a kasar China saboda ruwan da aka sheka kamar da bakin-kwarya ya lalata filin da za a murza ledar ta yadda ba za a iya yin wasa ba.

A ranar Lahadi ne kocin United Jose Mourinho ya bayyana filin na birnin Beijing da cewa "ba shi da kyau."

Haka kuma kafin a soke wasan, kocin City Pep Guardiola ya ce babbar bukatarsa ita ce kada 'yan wasansa su ji rauni.

Kungiyoyin biyu sun ce bakin "mutanen da suka hada wasa" ya zo daya wajen soke shi.

An yi hasashen za a ci gaba da sheka ruwa a ranar Litinin a birnin na Beijing.

Shi kansa jirgin da ya dauko wasu 'yan wasan sai da ya yi saukar gaggawa a Tianjin, mai nisan kilomita 160 daga Beijing sakamakon tsawar da aka rika yi a Beijing.

United za su koma Manchester ranar Litinin kamar yadda aka tsara, yayin da City za su tashi zuwa Shenzhen ranar Talata inda za su fafata da Borussia Dortmund ranar Alhamis.

Labarai masu alaka