Za a kara wa Afirka gurbi a gasar kofin duniya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mista Infantino yana so Afirka ta samu karin tawaga biyu da za su buga a gasar cin kofin duniya

Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa, Gianni Infantino, ya ce Afrika za ta iya kai wa zgayen karshe na gasar kwallon kafar duniya idan aka kara yawan tawagogin zuwa 40 nan da shekarar 2016.

Mista Infantino ya bayar da shawarar fadada tawagogin zuwa 32 kafin a zabe shi a matsayin shugaban hukumar a watan Fabrairu.

Yanzu haka dai kasashe biyar ne kawai ke da damar zuwa gasar cin kofin duniya daga Afrika.

Mista Infantino ya ce, ''Shawarata ita ce tawagogin Afrika su zama 40, kuma idan hakan ta tabbata Afrika za ta samu karin tawaga biyu da za su buga a gasar cin kofin duniya.''

Sai dai ba za a fara amfani da shawarar ba har sai shekarar 2026 inda aka riga aka tabbatar da cewa tawagogi 32 za su buga a gasar kofin duniya na 2018 a Rasha, da kuma ta 2022 a Qatar.

Labarai masu alaka