Klopp ya hukunta Sakho kan makara

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sakho tsohon dan kwallon Paris St-Germain

Kociyan Liverpool, Jurgen Klopp, ya umarci Mamadou Sakho ya koma gida, bayan dan kwallon ya makara zuwa sansanin horon kungiyar a Amurka.

An nuna wani faifan bidiyo a Liverpool a lokacin da Sakho ya makara, inda Telegraph ta ruwaito cewar Klopp din ya dauki matakin ladabtarwa ne kan dan kwallon.

Liverpool ba ta ce komai ba kan wannan rahoton, sai dai ta ce dan wasan mai tsaron baya zai je ya nemi magani kan raunin da yake yin jinya.

A cikin watannan ne hukumar kwallon kafa ta Turai, ta daina tuhumar Sakho kan amfani da kwayar da take kara kuzarin wasa.

Sakho ya koma Liverpool da murza-leda kan kudi fan miliyan 18 daga Paris St Germain a shekarar 2013.

Labarai masu alaka