Lyon ta ki sallamawa Arsenal Lacazette

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Lyon ba ta da niyyar barin dan kwallon ya bar kungiyar

Lyon ta ki sallama tayin da Arsenal ta yi wa dan wasanta Alexandre Lacazette na kudi fan miliyan 29 da dubu dari uku.

Lacazette, mai shekara 25, ya ci kwallaye 21 a wasanni 34 da ya buga gasar Faransa ta bana.

Sai a karshen kakar wasan 2019 ne, yarjejeniyar dan kwallon za ta kare da kungiyar ta Lyon.

Lyon ta karyata rahotannin da jaridu suka wallafa cewar ta ki amincewa da tayin sama da fan miliyan 42 daga tayin da Arsenal ta yi tun farko.