Barcelona ta dauki Gomes na Valencia

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Gomes shi ne dan kwallo na hudu da Barcelona ta dauka a bana

Barcelona ta dauki Andre Gomes, daga Valencia kan kudi fam miliyan 29 da 300,000.

Gomes mai shekara 22, ya koma kungiyar ne bayan da ya buga wa Portugal gasar cin kofin nahiyar Turai, wanda suka lashe a karon farko a tarihin kasar.

Dan kwallon shi ne na hudu da Barcelona ta saya a bana, bayan Samuel Umtiti daga Lyon Lucas Digne daga Paris St-Germain da kuma Denis Suarez daga Villarreal.

Haka kuma Barcelona ta sabunta yarjejeniya da Javier Mascherano, inda zai cigaba da yi mata wasa zuwa shekara biyar.

Mascherano mai shekara 32, ya buga wa Barcelona wasanni 247, tun lokacin da ya koma can da taka-leda daga Liverpool a shekarar 2010.

Labarai masu alaka