Ina da kwarewar yin aiki a Fifa - Samoura

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Samoura ita ce mace ta farko da ta rike babban ofishi a Fifa

Sakatariyar Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya, Fifa, Fatma Samoura, ta ce shekarun da ta yi tana aiki a yankunan da ake yin yaki ya taimaka mata wajen tunkarar kalubalen aikin hukumar.

Misis Samoura, 'yar Senegal, mai shekara 54, wadda ta yi aiki a majalissar dinkin duniya, ta fara aiki da hukumar Fifa a watan Yuni.

Sakatariyar ta shaidawa BBC cewar ta yi aiki a wuraren da ake fama da tashin hankali da suka hada da Afghanistan da Liberia da Saliyo da East Timor da Kosovo da kuma Nigeria.

Samoura ita ce mace ta farko da ta rike ofishin babbar sakatariya ta hukumar kwallon kafa ta duniya.

Ta kuma maye gurbin Jerome Valcke dan kasar Faransa, wanda aka dakatar daga shiga sabgogin tamaula shekara 12, bisa zargin aikata ba daidai ba a hukumar ta Fifa.

Labarai masu alaka