Mamelodi Sundowns ta ci Zamalek 1-0

Hakkin mallakar hoto callo getty
Image caption Sundowns ta kai wasan daf da karshe a gasar zakarun Turai

Mamelodi Sundowns ta Afirka ta Kudu ta kai wasan daf da karshe a gasar zakarun Afirka, bayan da ta ci Zamalek daya mai ban haushi a ranar Laraba.

A daya rukunin kuwa, Al Ahly ce ta doke Wydad Casablanca da ci daya da nema, hakan ya sa sai a wasan karshe za a tabbatar da kungiyar da ta kai wasan daf da karshe a gasar.

Zesco ta Zambiya ta buga kunnen doki 1-1 da Asec Mimosa, wanda hakan ya sa tana da maki iri daya da Wydad da kuma Asec Mimosas.

Rashin nasarar da Zamalek ta yi, yasa kociyanta Mohammed Helmi, ya yi murabus daga aikin, sannan an dakatar da kyaftin din kungiyar Hazem Emam kan cacar baki da ya yi da mambar kungiyar.