Schweinsteiger ya daina yi wa Jamus wasa

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Bastian Schweinsteiger ya taka muhimmiyar rawa a kwallon kafar Jamus

Kyaftin din Jamus Bastian Schweinsteiger ya bayyana cewa ya daina buga wa tawagar kasarsa kwallon kafa.

Dan wasan mai shekara 31, wanda ke murza leda a kungiyar Manchester United, na cikin 'yan kwallon da suka kai kasar ta dauki kofin kwallon kafa na duniya a Brazil a shekarar 2014.

Yana daya daga cikin 'yan wasan Jamus hudu da suka fi buga wa kasar wasanni, inda ya fito sau 120 - bayan Lothar Matthaus (150) da Miroslav Klose (137) da kuma Lukas Podolski (129).

Ya fara murza leda a kasashen duniya ne a shekarar 2004.

Labarai masu alaka