Marseille ta karbi aron Gomis

Hakkin mallakar hoto Getty

Dan wasan gaba na Swansea City Bafetimbi Gomis ya koma kungiyar kwallon kafar Marseille a matsayin aro.

Gomis, wanda ya tafi Swansea a shekarar 2014, ya dawo gasar Ligue 1 ta Faransa bayan ya taba wasa a Lyon.

Dan wasan, mai shekara 30, ya zura kwallaye bakwai a wasanni 35 da ya buga a kakar wasan da ta wuce, kuma shi ne dan wasan na uku da ya bar Swansea a wannan bazara.

Shi ma dan wasan Portugal Eder ya koma Lille, yayin da takwaransa na Italiya Alberto Paloschi ya koma Atalanta.

Rahotanni na cewa Marseille za ta rika bai wa Gomis cikakken albashi har tsawon lokacin da zai kwashe da ita.

Swansea kuwa ta sayi Mike van der Hoorn, Leroy Fer da kuma Mark Birighitti a kwanakin baya.

Labarai masu alaka